Wasanni - Super League

Muna kan shirin mu na Super League - Shugaban Barcelona

Kyallaye masu dauke da sunayen wasu fitattun kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar Turai.
Kyallaye masu dauke da sunayen wasu fitattun kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar Turai. © REUTERS/Nacho Doce

Shugaban kungiyar kwallon kafar Barcelona Joan Laporta ya dage cewa batun gasar 'Super League' mai cike da rudani na nan daram, duk da Allah wadai da akeyi da shirin.

Talla

Laporta ya bayyana hakan ne yayin taron mambobin kulob din inda ya yi ikirarin cewa gasar za ta rika samarwa Barcelona akalla euro miliyan 700 a kowace kaka, don haka bazasu bar batun yayi sanyi ba.

Duk da adawa daga UEFA da magoya baya da kuma kungiyoyin da ke hamayya, Laporta ya dage cewa Super League zata rika samar da karin kudin shiga mai daurewa ga club din tare da samar da gasa mai armashi .

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai dai ta dakatar da daukar matakin doka "har sai wani lokaci " a kan kungiyoyin uku dake yunkurin samar da gasar da zatayi hamayya da ta zakarun Turai Champions League.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.