Wasanni - Najeriya - Mexico

Super Eagles ta kira 'yan wasan cikin gida zalla don wasa da Mexico

Kocin tawagar Super Eagles ta Najeriya Gernot Rohr a sheklarar 2017.
Kocin tawagar Super Eagles ta Najeriya Gernot Rohr a sheklarar 2017. AFP/File

Kocin Super Eagles, Gernot Rohr, ya fitar da sunayen ‘yan wasa 25 da suka fito daga gida don fuskantar Mexico a wasan sada zumunci na kasa da kasa a filin wasa na Los Angeles Memorial Coliseum a ranar 4 ga watan Yuli.

Talla

Mai tsaron ragar Enyimba John Noble da dan wasan gaba Anayo Iwuala da kuma wani dan wasa mai suna Ikechukwu Ezenwa, mai tsaron ragar Heartland dake Ewere, su kan gaba a jerin sunayen ‘yan wasan da aka gayyata domin zuwa sansanin don wasan sada zumuncin.

Sauran wadanda aka gayyata sun hada da Ifeanyi Anaemena mai tsaron baya na Rivers United, dan wasan Enyimba Ekundayo Ojo da kuma ‘yan wasan gaba Ibrahim Olawoyin (Enugu Rangers) da Stephen Jude (Kwara United).

Ana saran ‘yan wasan su iso otal din Serob Legacy, dake Wuse, Abuja a ranar 22 ga watan Yuni tare da takardun tafiyarsu. 22 ne kawai daga cikinsu za su yi tafiya zuwa Amurka don wasan.

Manyan 'yan wasa Mexico

Dan wasan Atlético Madrid Héctor Herrera, Andrés Guardado da Diego Lainez na Real Betis, da PSV Eindhoven’s Erick Gutiérrez suna daga cikin manyan ‘yan wasan tsakiya da aka jera a wasannin sada zumuntar da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.