Wasanni - kwallon kafa

United zata baiwa Pogba kudin da ya fi kowa a Ingila

Dan wasan Manchester United Paul Pogba.
Dan wasan Manchester United Paul Pogba. Reuters/Jason Cairnduff

Manchester United na shirin yi dan wasanta na tsakiya Paul Pogba, mai shekaru 28 sabon tayin da yafi na kowane dan wasa a gasar Firimiyar Ingila da zai kai fam miliyan 104.

Talla

Chelsea kuwa na daf da sake sabunta kwantiragin N'Golo Kante, dan wasanta na tsakiya mai shekara 30, kuma ana sa ran ya samu kudi mai tsoka.

Dan wasan Chelsea N'Golo Kante
Dan wasan Chelsea N'Golo Kante AFP/File

Barcelona

Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar Memphis Depay da zarar kwantiraginsa ya kare a Olympic Lyon a karshen watan Yuni.

Dan kwallon tawagar Netherlands wanda yanzu haka ke buga mata gasar neman cin Kofin Turai.

Dan wasan Netherlands Memphis Depay yayin wasan su da Austria a wasan neman kofin Turai
Dan wasan Netherlands Memphis Depay yayin wasan su da Austria a wasan neman kofin Turai JOHN THYS POOL/AFP

Depay shi ne na hudu da Barcelona ta seya a bana bayan Sergio Aguero da Eric Garcia da kuma Emerson.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI