Birtaniya-Korona

Birtaniya ta sassauta dokar Korona saboda kwallon kafa

Filin wasa na Wembley
Filin wasa na Wembley JUSTIN TALLIS AFP

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa, za a kara yawan dandazon ‘yan kallo a filin wasa na Wembley zuwa fiye da dubu 60 a wasanni matakin gab da na karshe da kuma wasan karshe  na Gasar Cin Kofin Kasashen Turai ta Euro 2020.

Talla

Wannan na nufin cewa, ‘yan kallon za su mamaye akalla kashi 75  na kujerun da ake da su a filin wasan na Wembley.

Kazalika wannan karin adadin ‘yan kallon zai bai wa dandazon mutane damar yin tururuwa irinta ta farko a cikin watanni 15 domin kallon wani wasa a Birtaniya.

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Nahiyar Turai, Aleksander Ceferin ya bayyana facin cikinsa da wannan mataki na gwamnatin Birtaniya yana mai cewa, labari ne mai girma.

Da farko dai, an takaita yawan ‘yan kallo a  filin wasan na Wembley zuwa dubu 22 da 500 domin kallon wasannin Euro 2020 a matakin rukuni.

A bangare guda, wannan matakin na Birtaniya na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar  Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa, kasashe da dama na sassauta dokar yaki da cutar Korona saboda kwallon Kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.