Wasanni-Kwallon Kafa

Manchester city ta shirya biyan Fam miliyan 100 a kan Kane

Dan wasan Tottenham da Ingila, Harry Kane
Dan wasan Tottenham da Ingila, Harry Kane Glyn KIRK POOL/AFP

Manchester City ta shirya don zaffa neman dan wasan Totenham Harry Kane, inda yanzu haka  kungiyar, wadda ita ta lashe gasar Firimiya tana shirye shiryen taya dan wasan hukumance.  

Talla

Akwai rade radi daga majiyoyi kusa da kungiyar ta City da ke nuni da cewa kungiyar ta yi  tayin biyan fam miliyan 100 a kan dan wasan, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 139.

 Sai dai abin da ke dahir shine Manchester City na matukar bukatar dan wasan gaban na Ingila mai shekaru 27, duba da yadda Koch Pep Guardiola ya zaku ya sanya shi a cikin tawagarsa da ta lashe gasar Firimiya ta kuma kai wasan karshe na zakarun nahiyar Turai.

yanzu haka dai Harry Kane yana da sauran kwantiragi da kungiyar Tottenham da zai kai har shekarar 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.