Wasanni-Kwallon Kafa

Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zurawa Portugal kwallaye 109

Cristiano Ronaldo bayan zura kwallonsa a karawarsu da Faransa ta jiya laraba karkashin wasannin Euro.
Cristiano Ronaldo bayan zura kwallonsa a karawarsu da Faransa ta jiya laraba karkashin wasannin Euro. BERNADETT SZABO POOL/AFP

Bayan kwallaye 2 da ya zura a karawarsu da Faransa daren jiya Laraba karkashin wasannin gasar Euro, zuwa yanzu Cristiano Ronaldo na Portugal na da kwallaye 109 da ya zurawa kasarsa a manyan wasanni.

Talla

Kwallayen na Ronaldo a daren na jiya ya bashi damar gogewa ko kuma yin kan kan kan da Ali Daei dan wasan kasar Iran da ke matsayin dan wasa mafi zurawa kasarsa kwallo a tarihi.

Ronaldo mai shekaru 36, kwallayen nasa biyu a wasan na Portugal da Faransa da aka tashi wasa canjaras sun baiwa kasar damar tsallakawa zuwa rukunin kasashe 16 da za su fafata a gasa.

Tuni aka bayyana dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or har sau 5 a matsayin mafi nuna bajinta tsakanin takwarorinsa a wannan zamani.

Bayan karkare wasannin na jiya da suka matukar kayatar biyo bayan canjaras din duka kungiyoyin 4 da ke rukunin F, hukumar UEFA ta fitar da jadawalin yadda karawar gaba za ta gudana tsakanin kasashen 16.

Jadawalin na nuna cewa Wales za ta kara da Denmark a Amsterdam ranar Asabar 26 ga watan nan yayinda Italy za ta kara da Austria duk dai a makamanciyar ranar a London sai kuma haduwar Netherlands da Jamhuriyyar Czech a Budapest ranar Lahadi 27 ga wata kana Belgium da Portugal a Seville ranar 27 sai kuma wasan Faransa da Switzerland a Copenhagen ranar 28 ga watan nan sannan Ingila da Jamus a London ranar 29 ga watan na Yuli tukuna Sweden da Ukraine da za su hadu a Bucharest ranar 28 ga wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.