Spain - Wasanni

Spain ta janye dokar hana 'yan kallo shiga filayen wasanni

Filin wasan Camp Nou na kungiyar Barcelona dake gasar La Liga a Spain.
Filin wasan Camp Nou na kungiyar Barcelona dake gasar La Liga a Spain. © Reuters

Gwamnatin Spain ta janye dokar haramtawa ‘yan kallo kwarara cikin filayen wasanni a kasar, dokar da a baya aka kafa domin dakile yaduwar annobar Korona ta hanyar kaucewa cinkoson jama’a.

Talla

Cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin Spain ta ce a halin yanzu gwamnatoci a matakin yankunan kasar ne za su fayyace adadin 'yan kallon da za su baiwa idanunsu abinci kai tsaye a filayen wasanni, sai dai a yankin arewacin kasar akwai yiwuwar cigaba da tsaurara matakan hana cinkoson ‘yan kallon.

Matakin janye dokar hana ‘yan kallo shiga filaye a Spain cigaba ne mai muhimmanci da zai taimakawa kungiyoyin dake kasar musamman na kwallon kafa wajen farfadowa cikin sauri daga karayar tattalin arzikin da annobar Korona ta janyo musu.

A baya bayan nan ne dai shugaban gasar La Liga Javier Tebas ya ce yana sa ranz a a iya baiwa kashi 70 cikin dari na ‘yan kallo damar shiga filayen wasanni, idan aka saom sabuwar kakar wasa a cikin watan Agusta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.