Wasanni - UEFA

Zakarun Turai: UEFA ta daidaita darajar kwallayen gida da waje

Shugaban hukumar UEFA Alekander Ceferin.
Shugaban hukumar UEFA Alekander Ceferin. Fabrice COFFRINI AFP/Archives

Hukumar kwallon kafa ta UEFA ta daidaita darajar kwallayen gida da waje a gasar zakarun Turai, matakin da ta ce zai soma aiki a sabuwar kakar wasan da za a shiga ta 2021/2022.

Talla

Matakin UEFA na nufin daga yanzu idan kungiyoyi suka yi kankankan wajen cin kwallaye yayin fafatawarsu a gida da waje, za a basu karin mintuna 15 ne domin sake karawa, idan kuma damar ta faskara sai a kai zagayen bugun fanareti, wato daga kai sai mai tsaron raga.

Sanarwar da shugaban hukumar ta UEFA Aleksander Cefrin ya fitar a ranar yau Alhamis ta kawo karshen muhwarar da aka share shekaru ana yi kan rashin adalcin da wasu ke zargin na tattare da dokar daga darajar kwallayen da kungiya ke ci a wajen gidanta.

Tun a shekarar 1965 ake amfani da dokar banbanta darajar kwallayen gida da waje a gasar cin kofin zakarun Turai, lokacin da ake kiran gasar da European Cup a turance, kafin daga bisani a sauya sunan gasar zuwa Champions League a kakar wasa ta 1992 zuwa 1993.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.