Wasanni-Euro

Ingila za ta yi taka-tsan-tsan yayin wasanta da Jamus- Henderson

Dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson
Dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson Carl Recine POOL/AFP

Dai dai lokacin da ake shirin faro wasannin zagayen kasashe 16 na gasar Euro, dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson ya bayyana haduwarsu da Jamus ranar talata a matsayin mai cike da kalubale.

Talla

A cewar Henderson wanda shi ne kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Liverpool wasan ba zai zowa Ingila da sauki ba, la’akari da yadda kasar ta saba shan kaye hannun Jamus a irin wannan mataki.

Sai dai Henderson ya ce baya fatan tarihin ya maimaita irin rashin nasarar da suka yi hannun Jamus din a 1996 lokacin da kasashen 2 suka karar da mintunan wasansu ba tare da kwallo ba wanda ya kai ga bugun fenariti kuma Ingilar ta sha kaye.

Wasan a wannan karon zai gudana ne gaban ‘yan kallo dubu 40 a filin Wembley da ke London wanda Henderson ke cewa zai zama abin alfahari idan har tawagar ta su ta iya lallasa Jamus a tsakar London.

Cikin shekaru 31 wannan ne karo na 4 da kasashen biyu za su hadu da juna a rukunin kwaf daya, kuma dukkanin ukun da suka gabata Jamus ke nasara da suka kunshi haduwar 1996 wadda Jamus ta lashe kofin na Euro sai haduwar 1990 da ta 2010 dukka a gasar cin kofin Duniya.

Baya ga Henderson masu sharhi kan harkokin wasanni na ci gaba da tsokaci kan haduwar wadda za ta ja hankali matuka, inda Alan Shearer ke cewa babu wata fargaba ga Ingila game da karawar, a bangare guda kuma Lothar Matthaus tsohon dan wasan Jamus ke cewa Ingilar ka iya nasara a karawar idan har bata kai ga bugun fenariti ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.