Wasanni-Euro

Mutane sun fi son Denmark ta yi nasara kanmu saboda Eriksen- Wales

Tawagar 'yan wasan kwallon kafar Wales bayan samun gurbi a zagayen kasashe 16 na cin kofin kasashen Turai Euro.
Tawagar 'yan wasan kwallon kafar Wales bayan samun gurbi a zagayen kasashe 16 na cin kofin kasashen Turai Euro. GEOFF CADDICK AFP

Mai tsaron baya na tawagar kwallon kafar Wales Conor Roberts ya ce yana da masaniyar cewa kashi 99 cikin dari na masu kallon wasannin Euro na son tawagar Denmark ta yi nasara kansu yayin haduwarsu ta gobe asabar a Amsterdam.

Talla

Duk da cewa tawagar ta Wales na gaban Denmark a wasannin na Euro kama daga yadda kowacce ta iya fitowa daga rukuninta zuwa zagayen kasashen 16 dama yawan kwallayen da kowacce ta zura amma Roberts ya ce tausayawar duniya kan rashin lafiyar Christian Eriksen ya sa Denmark din samun fifikon fatan ta yi nasarar dage kofin fiye da kowacce kasa.

A cewar Conor Roberts da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Swansea a Ingila za su iyakar kokarinsu wajen ganin goyon bayan da Denmark ke da shi bai karya musu gwiwa ba a haduwar.

Tun bayan faduwar Christian Eriksen sakamakon bugawar zuciya lokacin da ake tsaka da wasan farko na gasar tsakaninsu da Finland ne, tawagar ta Denmark ta saye zukatan masoya kwallo musamman ganin yadda suka tsayar da wasan tare da katange dan wasan nasu gabanin kai masa daukin gaggawa.

Duk da cewa Eriksen na ci gaba da murmurewa a gida bayan sallamo shi daga asibiti, amma kwarin gwiwa da goyon bayan da tawagar kasar tasa ke samu na bata damar ci gaba da nuna bajinta a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.