Ingila-kwallon kafa

Ingila ta goge tarihin shekaru 55 bayan lallasa Jamus a gasar Euro

Harry Kane bayan nasarar zura kwallo a karawarsu da Jamus karkashin gasar Euro.
Harry Kane bayan nasarar zura kwallo a karawarsu da Jamus karkashin gasar Euro. Andy Rain POOL/AFP

Nasarar Ingila kan Jamus ya bai wa tawagar ta Gareth Southgate damar goge tarihin shekaru 55 da aka shafe ta na shan kaye hannun Jamus galibi a makamantan wannan wasa.

Talla

Raheem Sterling na Manchester City da Harry Kane na Tottenham ne suka zurawa 3 Lions kwallayenta biyu gaban ‘yan kallo dubu 40 da suka shiga filin wasa na Wembley a birnin London, nasarar da ke matsayin gagarumin abin alfahari ga hatta tsaffin ‘yan wasan tawagar ta Ingila.

Shekaru 55 aka shafe Ingila na shan kaye a hannun Jamus yayin manyan wasa musamman a irin wannan mataki na kwab daya, ciki kuwa har da wasanni 2 a gasar cin kofin Duniya na baya-bayan nan da kuma gasar Olympics da sauran manyan wasanni.

Tuni dai masu sharhi kan wasanni suka fara tsokaci kan ruwan idon da a baya ake ganin Gareth Soutgate ya rika yi gabanin tantance ‘yan wasan da za su wakilci kasar a gasar ta Euro, yayinda suka jinjinawa Jordan Pickford wanda har zuwa yanzu ba a zura masa ko da kwallo guda a gasar ba.

Ko a wasan dai Timo Werner da Kai Havertz sun rika kai farmaki amma mai tsaron ragar na Ingila Pickford ya hanasu kai labari, inda aka tashi wasa Ingilar na da 2 Jamus babu ko daya.

Ingilar dai za ta hadu da ko dai Ukraine ko kuma Sweden don buga zangon wasan gab da na kusa da karshe na gasar a juma’a mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.