Messi ya kafa tarihi, ya nuna bajinata a wasan Argentina da Bolivia
Wallafawa ranar:
Lionel Messi ya kafa sabon tarihin na wanda ya fi buga wasanni a babbar tawagar kwallon kafar Argentina tare da nuna bajinta, inda da ya ci kwallaye 2 bayan ya taimaka an ci guda kafin hutun rabin lokaci a fafatawa tsakaninsu da Bolivia, a wasa ta 148 da ya buga wa kasarsa.
Da wannan wasa da Messi ya buga wa Argentina, ya zarce Javier Mascherano da yawan wasanni a matakin rukuni a gasar Copa America, ya kuma ci kwallaye 75 a tawagar kwallon kafar kasarsa.
Argentina ta jagoranci wannan rukuni na A bayan da ta yi nasara 4-1 a kan Bolivia, kuma za ta gwabza da Ecuador a wasan daf da kusa da karshe.
A wannan wasa dai Messi shi ya fi kowa cin kwallaye, shi kuma ya fi taimakawa aka kai ga nasara.
Messi ya yi wasan ne a matsayin mai raba kwallaye, da kuma mai cin kwallaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu