Wasanni-Kwallon Kafa

Tottenham ta nada Nuno Espirito Santo matsayin Manaja

Nuno Espirito Santo sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham
Nuno Espirito Santo sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Andy Rain POOL/AFP/File

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta sanar da nadin Nuno Espirito Santo a matsayin mai horar da tawagarta kan kwantiragin shekaru 2 da nufin maye gurbin Maurinho da ta kora a watan Aprilu.

Talla

Nuno Espirito wanda ya jagoranci Wolves tsawon kaka 4 tare da nuna bajinta, Tottenham na ganin zai iya cire mata kitse a wuta bayan jerin rashin nasara da ta rika ganin a kakar wasannin da suka gabata ta baya-bayan nan.

Bayan tafiyar Mourinho Tottenham ta yi amfani da Ryan Mason mai shekaru 29 da ya jagoranci tawagar zuwa karshen kakar da ta gabata.

Da ya ke sanar da matakin a shafinsa, Nuno ya bayyana horar da tawagar Tottenham a matsayin abin alfahari gare shi.

Kafin yanzu dai Tottenham ta yi zawarcin tsohon kocin AS Roma Paulo Fonseca bayan gaza cimma jituwa da Nuno a farko.

Haka zalika kungiyar wadda ta rasa sukunin taka leda a gasar cin kofin zakarun Turai na kaka mai zuwa, ta yi kokarin dawo da tsohon manajanta Mauricio Pochettino da ke jagorancin PSG a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.