Wasanni - kwallon kafa

Ramos ya bayyana dalinsa na komawa PSG da taka leda

Dan wasan baya na kasar Sifen kuma tsohon Kaftin din Real Madrid Sergio Ramos da ya komawa kungiyar Paris Saint-Germain don ci gaba da taka leda a gasar Ligue 1 na Faransa. à Abou Dhabi 15 ga watan Dismaba 2017.
Dan wasan baya na kasar Sifen kuma tsohon Kaftin din Real Madrid Sergio Ramos da ya komawa kungiyar Paris Saint-Germain don ci gaba da taka leda a gasar Ligue 1 na Faransa. à Abou Dhabi 15 ga watan Dismaba 2017. Giuseppe CACACE AFP/Archives

Shahararren dan wasan baya na kasar Sifen kuma tsohon Kaftin din Real Madrid Sergio Ramos ya bayyana dalilansa na komawa kungiyar Paris Saint-Germain don ci gaba da taka leda a gasar Ligue 1 na Faransa.

Talla

Da yake kare matakin, Ramos yace abin alfahari ne kasancewa a kungiya kamar PSG mai dauke da fitattun ‘yan wasa kuma daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniyar tamola, don haka yana murnar kasancewarsa a Faransa.

Dan wasan mai shekaru 35 da ya koma Madrid daga Sevilla tun yana matashi, kuma ya kashe kakar wasanni har 16, yace burinsa shine ganin PSG ta kai ga gaci a manyan gasannin kwallon kafa a duniya.

A makon da ya gabata ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu da PSG kuma ana saran ya taimaka mata lashe kambin farko na gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.