Kwallon Kafa

Ba za a maimata abin kunyar da ya faru ba- FA

Wasu daga cikin magoya bayan Ingila
Wasu daga cikin magoya bayan Ingila Niklas HALLE'N AFP

Hukumar Kwallon Kafar Ingila ta ce, ta dukufa wajen tabbatar da cewa, ba sake maimaita abin kunyar da aka aikata a yayin wasan karshe a Gasar Cin Kofin Kasashen Turai ta Euro 2020.

Talla

Hukumar ta FA ta ce, za a gudanar da bincike mai zaman kansa game da yadda aka keta matakan tsaro a yayin wasan.

Magoya bayan Ingila sun yi arangama da jami’an tsaro a yayin yunkurinsu na kutsawa cikin filin wasan na Wembley a ranar 11 ga watan nan na Yuli duk da cewa ba su sayi tikiti ba.

Tuni Hukumar Kwallon Kafar Turai ta UEFA ta gabatar da tuhume-tuhume guda hudu ga Hukumar Kwallo Kafar Ingila kan wannan muguwar dabi’ar da magoya bayan suka nuna.

Daga cikin abin da magoya bayan na Ingila suka aikata har da jefe-jefe da karikitai da kunna tartsatsin wuta da kuma yin ihu a lokacin da ‘yan wasan Italiya ke rera taken kasarsu gabanin soma karawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.