Wasanni - Olympic

Tawagar 'yan wasan Olympic ta Najeriya ta isa Tokyo

Tawagar 'yan wasan Olympic ta Najeriya ta isa Tokyo
Tawagar 'yan wasan Olympic ta Najeriya ta isa Tokyo © ©Nigeria news daily

Tawagar ‘yan wasan Najeriya da zata wakilci kasar a wasannin Olypic ta isa masauikin Wasanni dake birnin Tokyo na kasar Japan gabanin bikin bude gasar ta Tokyo 2020 ranar Jumma’a 23 ga wannan wata na Yulin a filin wasa na Olympic da ke Tokyo.

Talla

'Yan wasan Najeriya da ke sansanin yanzu haka da suka hada da: wasan kwallon tebur, da na motsa jiki, sai kuma wasan damben taekwondo da kuma na tsere.

Rukunin farko, wanda ya kunshi ‘yan wasa biyu, masu horarwa biyu da jami’ai shida, sun bar Abuja a ranar 6 ga watan Yuli, yayin da rukuni na biyu ya isa sansanin horonsu da ke Kisarazu a ranar Laraba.

Rukuni na uku na 'yan wasa, wadanda suka kunshi' yan wasan badminton da suka bar Najeriya a ranar 17 ga watan Yuli, za su hade da kungiyar a bayan an duba lafiyarsu.

Rukunin karshe, wanda zai hada da ministan wasanni, Sunday Dare, zai bar Najeriya a ranar 19 ga watan Yuli, yayin da kungiyoyin kwallon kwando maza da mata za su hade da tawagar Amurka zuwa Tokyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.