Kwallon Kafa

An kama dan wasan da ke lalata kananan yara

Kwallon Kafa
Kwallon Kafa Patrick Smith GETTY IMAGES NORTH AMERICA/AFP

Wani dan wasan firimiyar Ingila ya shiga hannun jami’an ’yan sandan Birtaniya bisa zargin sa da laifin lalata da kananan yara.

Talla

Dan wasan mai shekaru 31 wanda kawo yanzu ba a bayyana sunansa ba saboda dalilai na shari'a, an tsare shi ne a ranar Juma’ar da ta gabata a Greater Manchester.

A cikin wata sanarwa, kungiyar da dan wasan ke taka mata leda, ta tabbatar da cafke shi, tana mai cewa, a shirye take ta taimaka wa hukumomi wajen gudanar da bincike.

Kodayake tuni aka bayar da belin dan wasan kafin a ci gaba da tuhumar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.