Wasanni - Olympic

An bude wasannin gasar Olympics cikin tsauraran matakan korona

Wasu masu sanya da kellen rufe hanci da baki a filin wasannin Olympics na Tokyo 2020 a birnin Tokyo na kasar Japan, ranar 8 ga watan Yuli 2021.
Wasu masu sanya da kellen rufe hanci da baki a filin wasannin Olympics na Tokyo 2020 a birnin Tokyo na kasar Japan, ranar 8 ga watan Yuli 2021. AP - Shinji Kita

A ranar Laraba aka fara gudanar da gasar wasannin Olympics ta Tokyo ,ba tare da 'yan kallo ba. Wannan na zuwa ne dai bayan shekara guda da dage gasar, sakamakon bullar annobar Covid-19 da ta haifar da illoli masu tarin yawa a bangarori da dama ciki, har da harkokin wasanni.

Talla

Bikin bude wasannin Olympic 2020 na Tokyo zai gudana ne a ranar Juma'a wato 23 ga Yuli, sai dai bikin budewar babu taron jama’a ko kuma wasan wuta da kuma ‘yan rawa da aka saba yi.

Kamar yadda bayanai ke cewa hatta masu kamfanonin da ke daukar nauyin wasanni ba zasu halarci wurin bikin ba, bayan da suka zuba sama da dala biliyan uku a gasar.

Wannan gasa dai ta zo ne a dai-dai lokacin da duniya ke cikin tsaka mai wuya saboda annobar Corona, inda yanzu haka a kowacce rana akan yiwa ‘yan wasa gwajin cutar domin kaucewa yaduwarta, bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi akai.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa mambobin kwamitin shirya gasar cewa babu tabbacin cewa ba za a samu yaduwar cutar ba, la’akari da irin tasirin da take da shi.

Duk da haramcin da aka yiwa 'yan kallo a mafi yawan wuraren wasannin Olympics din, wasu magoya baya sun sami damar kallon wasanni a zagayen farko dai..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.