Kwallon Kafa

Sancho ya koma Manchester United

Jadon Sancho
Jadon Sancho Paul ELLIS AFP

Dan wasan Ingila Jadon Sancho ya kammala sauya shekarsa zuwa Manchester United akan farashin Pam miliyan 73 daga Borussia Dortmund, inda ya ce, burinsa na rayuwa ya cika.

Talla

Sancho ya zama dan wasan Ingila na biyu mafi tsada da aka saya a tarihin, bayan Harry Maguire wanda shi ma ke taka leda a Manchester United da ta sayo shi kan Pam miliyan 80.

Sabon dan wasan na Manchester United mai shekaru 21 zai shafe shekaru biyar yana murza wa kungiyar tamola a karkashin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma.

Tun a kakar bara ne Manchester United ke ta hankoron sayo Sancho, amma abin ya ci tura sakamakon rashin jin jituwa kan farashinsa

Sancho ya zazzaga kwallaye 50 a raga tare da taimaka wa wajen zura 57 a cikin jumullar wasanni 137 da ya buga wa Dortmund.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.