Wasanni-Kwallon Kafa

Varane ya amince da yarjejeniyar buga wa Manchester United wasa zuwa 2026

Raphael Varane, dan wasan Real  Madrid.
Raphael Varane, dan wasan Real Madrid. © GABRIEL BOUYS AFP/File

Rahotani na cewa Raphael Varane ya amince da yarjejeniyar kwantiragin buga wa Manchester United wasa zuwa 2026, amma ba a kai ga cimma yarjejeniya da Real Madrid a kan dan wasan bayan ba.

Talla

Har yanzu dai Manchester United ba su kai ga tayin Varane  a hukumance a gun Real Madrid ba, amma suna bibiya ganin sun samu amincewar dan wasa, kuma kungiyar ta kasar Spain sun amince dan wasan na iya barin Santiago Bernabeu.

Ba a sa ran canza sheka, kuma Varane, wanda yake matukar girmama Madrid bai mika bukatar barin kungiyar ba, saboda ya gwamnaci ya yi ta jira  har  sai an warware batun makomarsa.

Ganin cewa kwantiragin Varane, wanda ya shafe shekaru 10 a kungiyarsa zai kare  a shekarar 2022, akwai bukatar Madrid ta  dau matakin sabantawa ko kuma ta yi hannun riga da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI