Wasanni-Kwallon Kafa

Griezmann yana neman canza sheka zuwa Juventus

Antoine Griezmann scored both goals in Barcelona's come-from-behind win at Villarreal, and the Catalans are well-placed now to pip Atletico Madrid to the Spanish title
Antoine Griezmann scored both goals in Barcelona's come-from-behind win at Villarreal, and the Catalans are well-placed now to pip Atletico Madrid to the Spanish title JOSE JORDAN AFP

 Dan wasan gaba na Barcelona, Antoine Griezmann ya zaku ya koma kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ke wasa a birnin Turin na Italiya.

Talla

Juventus ta riga ta yi tuntubi  Barcelona a game da yiwuwar komawar dan wasan kasar Faransan Turin.

Barcelona sun nuna alamun cewa sun shirya sayar da Griezmann duba da yadda suka rage mai albashi, kana suka sake shiga yarjejeniya da kaftin din kungiyar Lionel Messi.

Dan wasan wanda yake zaman jiran makomarsa a Barcelona ya kwana da sanin cewa ba shi da gurbi a tawagar kungiyar.

 Bugu da kari, akwai matsalar kudi a Barcelonar, wadda take cikin nazari a kan yadda za ta yi da albashin Messi mai tsoka, duba da sanya hannu a sabon kwantiragi da ya yi kwanan nan.

Duk da kakar wasa biyu maras armashi a Camp Nou, tsohon dan wasan na Atletico bai rasa kungiyoyin da ke zawarcinsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.