Wasanni-Kwallon Kafa

Man United na daf da cimma yarjejeniyar sayo Varane daga Real Madrid

dan wasan baya na Faransa da Real Madrid, Rafael Varane.
dan wasan baya na Faransa da Real Madrid, Rafael Varane. FRANCK FIFE AFP/Archives

Manchester United na daf da cimma yarjejeniyar sayen dan wasan baya na Real Madrid, Raphael Varane, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Talla

A  farkon makon nan  dai kungiyoyin biyu ba su kai ga cimma matsaya ba, amma sun yi aiki tukuru daga baya don dinke barakar da aka samu a tsakaninsu, inda yanzu ake sa ran kai wa matsaya a kan fam miliyan 39, kwatankwacin dala miliyan 53.

Tun bayan da Manchester United suka kammala sayen Jadon Sancho daga Borussia Dortmund, suka kara azama a wajen kokarin kawo Varane kungiyar.

An samu ci gaba sosai a game da yarjejeniyar tsakanin Man United da Real Madrid a kan dan wasan, kuma ana fata nan gaba kadan a cikin wannan mako za a ci gaba da tattaunawa.

Da farko dai ana tunanin United tana so ta yi amfani da damar cewa Varane yana da saura shekara daya ne kawai ya karkare kwantiraginsa, don matsa wa Madrid lamba ta yi mai yiwuwa da wuri gudun kada dan wasan ya tafi ga banza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.