Wasanni-Kwallon Kafa

Real Madrid za ta wa Isco kora da hali

Santiago-Bernabeu, filin wasan Real Madrid.
Santiago-Bernabeu, filin wasan Real Madrid. AFP/Archives

 Rahotanni na nuni da cewa ba za a bai wa dan wasan tsakiya na Spain, Isco sabon kwantiragi a Real Madrid ba.

Talla

Dan wasan mai shekaru 29 na daf da zama babu wata igiyar yarjejeniya a kansa, inda a shekarar 2022 ne kwantiraginsa zai kare, kuma yana da damar barin Santiago Bernabeu a wannan bazara, duk da cewa Carlo Ancelotti ya dawo a kungiyar a karo na biyu a matsayin  mai horarwa.

Sau 10 ne kawai aka fara wasa da Isco a dukkan gasanni a karkashin mai horarwa, Zenedine Zidane a kakar wasa ta 2020-21, kuma ana danganta shi da komawa gasar Firimiyar Ingila.

Zuwan Ancelotti bai canza komai ba a game da abin da Isco ke fuskanta a Real Madrid ko kadan. Kungiyar na ta kokarin sayar da  dan wasan da ya taho daga Malaga don kauce wa yanayin da zai sa ya bar kungiyar ba tare da ta samu ko sisin kwabo ba a lokacin da kwantiraginsa zai kare a shekarar 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.