Wasanni-Kwallon Kafa

Barcelona da Neymar sun sasanta rikicinsu cikin ruwan sanyi a wajen kotu

Neymar JNR. dan wasan PSG.
Neymar JNR. dan wasan PSG. NORBERTO DUARTE AFP/Archives

Barcelona da Neymar sun sansanta rikcin da suka dade suna yi a kotu cikin ruwan sanyi, kamar yadda kungiyar kwallon kafar ta kasar Faransa ta bayyana, inda yanzu shari’ar da suka shafe shekaru 4 suna yi a kotu ya kawo karshe.

Talla

Shahararren dan wasan kasar Brazil din ya fara yi wa Barcelona ne wasa kafin kungiyar PSG ta saye a kan kudi da ya kai fam miliyan 200 a bazarar shekarar 20217.

Neymar ya yi korafin cewa yana bin Barcelona bashin wasu kudaden alawus alawus duk da cewa ya bar kungiyar, inda ita ma Barcelonar ta yi ikirarin cewa ya saba yarjejeniyar da suka kulla da shi.

A yanzu dai Barcelona ta wallafa a shafinta na intanet cewa sun sasanta da dan wasa a wajen kotu, cikin ruwan sanyi da dan wasa, Neymar da Silva Santos Junior.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.