Wasanni-Kwallon Kafa

Manchester United ta amince da sayen Varane kan fam miliyan 41 daga Madrid

Raphael Varane controla un balón con el pecho durante el partido liguero entre el Real Madrid y el Alavés disputado el 10 de julio de 2020 en la capital española
Raphael Varane controla un balón con el pecho durante el partido liguero entre el Real Madrid y el Alavés disputado el 10 de julio de 2020 en la capital española AFP/Archivos

Manchester United ta amince da yarjejeniyar sayen dan wasan baya, Raphael Varane daga Real Madrid, kamar yadda rahotanni da ke fitowa daga birnin Madrid ke bayyanawa.

Talla

Varane zai kasance babban kamu na 2 da United ta yi a wannan bazara, biyo bayan zuwa Jadon Sancho daga Brussia Dortmund tun da farko a kan fam miliyan 73.

A cikin karshen makon da ya gabata an samu ci gaba a tattaunawar da kungiyoyi biyu da dan wasan suke yi a kan abin da za  a biya dan wasan, kuma an karkare da Real Madrid a ranar Litinin a kan farashi.

Rahotanni sun bayana cewa United za ta biya kudin da ya kai fam miliyan 41 ne a kan wannan dan wasa.

A halin da ake ciki, Real Madrid za ta biya wani kudi da ya kai fam miliyan 1 ga tsohuwar kungiyar dan wasan ta Faransa wato Lens a matsayin ladan goyon baya.

Yanzu gwajin lafiya dan wasan yake jira don tabbatar da ciniki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.