Wasanni-Kwallon Kafa

Ronaldo zai ci gaba da zama a Juventus

Dan wasan gaban Juventus Cristiano Ronaldo yana amsa gaisuwar magoya baya, a lokacin da ya isa birnin Turin don gwajin lafiyarsa.
Dan wasan gaban Juventus Cristiano Ronaldo yana amsa gaisuwar magoya baya, a lokacin da ya isa birnin Turin don gwajin lafiyarsa. MIGUEL MEDINA AFP

Cristiano Ronaldo ya koma atisaye a Juventus bayan jita jitar da ta mamaye makomarsa a kungiyar da ke birnin Turin ta kasar Italiya.

Talla

Dan wasan mai shekaru 36 ya samu jinkiri a shirye shiryen tinkarar kaka mai zuwa sakamakon wakiltar kasarsa Portugal da ya yi a gasar cin kofin kasashen nahiyar Turai ta Euro 2020.

An yi ta cece kuce da hasashe a game da inda dan wasan da ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya har sau 5 zai murza tamaula a kaka mai zuwa, amma sai gashi ya koma ci gaba da zama a  gasar Serie A.

A ranar Lahadi ne ya koma Turin, bayan hutun da ya biyo bayan karkare gasar zakarun nahiyar Turai.

Ronaldo ne ‘yan kallo suka fi mayar da hankali a kansa a lokacin da tawagar Juventus ta shiga filin atisayenta a birnin Turin a  jiya Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.