Wasanni-Olympic

Zan mayar da hankali kan lafiyata-Biles

 Simone Biles
Simone Biles Loic VENANCE AFP

‘Yar wasan guje-guje da tsalle-tsalle da ta lashe zinari har sau hudu a wasannin Olympics wato Simone Biles ta Amurka ta bayyana cewa, za ta mayar da hankali kan lafiyar kwakwaluwarta bayan ta fice daga gasar Olympics ta Tokyo 2020.

Talla

Ana tsaka da wasan na Oluympics ne,  Biles ta ce ta janye kafin a  kammala, lamarin da ya bai wa 'yan kallo mamaki.

Matashiyar ‘yar wasan mai shekaru 24, ta samu sakamako mafi karanci a tarihinta na wasannin olympics bangaren lankwashe-lankwashe, inda ta samu 13.766.

Ita ce ‘yar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta Amurka da ta fi yawan lambobin yabo a wannan bangaren, sannan tana cikin ‘yan wasan da hankula suka karkata a kansu a Tokyo 2020 da ke gudana a Japan.

A wani labarin kuma, an yi waje da shahararriyar ‘yar wasan kwallon Tennis lamba daya a duniya bangaren mata,  wato  Naomi Osaka ta Japan  a gasar wasannin na Olympics.

Osaka ta sha kashi ne a gida a hannun ‘yar wasan Tennis ta kasar Czech Marketa Vondrousova.

Osaka mai shekaru 23 tana cikin ‘yan wasan da suka tallata wannan gasa ta Tokyo 2020, har ma ta samu karramawar kunna wutar gasar a bikin bude ta a makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.