Wasanni-Kwallon Kafa

Paris Saint Germain na take-taken dauko Pogba

Paul Pogba dan wasan Manchester United.
Paul Pogba dan wasan Manchester United. PETER CZIBORRA POOL/AFP/File

Paris Saint-Germain ta fara tattaunawa da dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba don tantance ko yana da sha’awar canza sheka a wannan kaka.

Talla

Ana ganin babbar kungiyar wasan kwallon kafar ta kasar Faransa na iya tayin  Pogba a hukamance a cikin makonni masu zuwa, sai dai ba su kai ga yanke shawarar sayensa a wannan kaka ba, ko kuma za su bari ne zuwa shakara mai zuwa a lokacin da kwantiraginsa zai kare da United.

Kwantiragin Pogba na yanzu zai kare ne  bazarar shekarar 2022, wato abin da hakan ke nufi shine yana iya tattaunawa da wata kungiya a watan Janairu a kan batun sauya sheka.

A makon da ya gabata ne jaridar Daily Mirror ta Birtaniya ta wallafa labarin da ke cewa Pogba ya yi watsi da kunshin kwantiragin da Manchester United ta mika mai na tsawaita zamansa a kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.