Wasanni

Arsenal ta sayo sabon dan wasan baya

Ben White rike da kwallo
Ben White rike da kwallo Gareth Fuller POOL/AFP

Arsenal ta sayo dan wasan baya na Ingila, Ben White daga Brighton akan farasahin Pam miliyan 50.

Talla

Dan wasan mai shekaru 23 ya amince da yarjejeniyar zaman dogon zango a filin wasa na Emirates.

Tun a watan jiya ne Arsenal ta amince da wannan yarjejeniuya karkashin wasu ka’idoji, amma sauyin shekar dan wasa ya kammalu ne bayan dawowarsa daga hutu.

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayyana cewa, da ma sun dana tarkonsu akan Ben don sayo shi kuma suna alfahari da kulla wannan ciniki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.