Wasanni-Olympic

Djokovic ya gaza kafa tarihi a Olympic

Novak Djokovic,
Novak Djokovic, Tiziana FABI AFP

Burin Novak Djokovic na lashe zinari a gasar Olympic ya kawo karshe bayan ya yi rashin nasara a hannun Alexandre Zverev a wasan kwallon Tennis, matakin wasan gab da na karshe.

Talla

Djokovic wanda shi ne lamba daya a duniyar kwallon Tennis, ya yi burin kafa tarihin zama dan wasan na miji na farko da ya lashe daukacin manyan gasa hudu na kwallon Tennis da kuma lambar yabo ta zinari a gasar Olympic  duk a cikin shekara guda.

Sai dai Zverev na Jamus ya yi masa haramiyar kafa wannan tarihin sakamakon doke shi da ya yi a birnin Tokyo.

Yanzu haka Zverev mai shekaru 24, zai kara da Karen Khachanov na Rasha a ranar Lahadi mai zuwa a wasan karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI