Wasanni-Kwallon Kafa

Italiya za ta binciki zargin nuna wariyar da aka yiwa Kalidou Koulibaly

Dan wasan Napoli Kalidou Koulibaly.
Dan wasan Napoli Kalidou Koulibaly. Alberto PIZZOLI AFP

Hukumar kwallon kafar Italiya ta bude bincike kan zargin nuna wariyar da magoya bayan Fiorentina suka yiwa mai tsaron bayan Napoli Kalidou Koulibaly yayin wasan kungiyoyin biyu a shekaran jiya lahadi karkashin gasar Serie A.

Talla

Baya ga Koulibaly ‘yan wasan Napoli irinsu Victor Osimhen da Frank Zambo dukkaninsu sun fuskanci kalaman wariyar da magoyan bayan na Fiorentina suka rika rerawa a wake bayan nasarar Napoli a karawar da kwallaye 2 da 1.

Kwamitin da hukumar kwallon kafar ta Italiya ta kafa zai yi tattaki zuwa Fiorentina don fara bincike kan batun baya ga faya-fayan bidiyo da kwamitin zai yi amfani da su don tabbatar da zargin.

Baya ga hukumar kwallon kafar, shi kansa ofishin babban mai shigar da kara na Italiya ya bude bincike kan batun, matakin da ke zuwa bayan tsanantar wariyar da ‘yan wasa bakar fata ke fuskanta a nahiyar ta Turai duk da ikirarin hukumomi na magance matsalar.

Dan wasan na Senegal wanda ya matukar fusata da abin da magoya bayan na Forentina suka yi masa har ta kai ga shigar da kara, ya bukaci zartas da hukuncin dakatarwar har abada ga duk wanda aka samu da laifin rera masa waken na nuna wariya.

Wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram ya bayyana yadda magoya bayan ke kiransa da dan biri a duk lokacin da ya dauki kwallo, inda ya ce irin wadannan mutane sam basu cancanci ci gaba da kasancewa a filin wasanni ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI