Wasanni-Kwallon Kafa

Salah na shirin goge tarihin da Didier Drogba ya kafa a Firimiya

Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah.
Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah. Paul ELLIS AFP

Dan wasan gaba na Masar da ke taka leda a Liverpool Mohamed Salah na gab da goge tarihin da Didier Drogba na Ivory Coast ya kafa a gasar firimiyar Ingila.

Talla

Drogba wanda ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea shi ne dan wasan Afrika mafi zura kwallo karkashin gasar ta Firimiyar Ingila inda ya ke da yawan kwallaye 104 a zamanin taka ledarsa.

Yanzu haka Mohammed Salah na Masar na da kwallaye 103 da ya zura karkashin wasannin gasar ta Firimiya bayan kwallonsa a wasan da suka yi canjaras da Manchester City da kwallaye 2 da 2 a karshen mako.

Dan wasan na Masar mai shekaru 29 kwallo guda daya cal ya rage masa ya kamo Drogba.

Masana wasanni na ci gaba da kwatanta tauraron na Liverpool da manyan 'yan kwallo irinsu Ronaldo da Messi musamman bayan kwallonsa a wasan Liverpool na ranar lahadi wadda aka bayyana da mafi kayatarwa a kaf kwallayen firimiya.

Mohamed Salah dai na ci gaba da nuna bajinta a wasannin Liverpool tun bayan sayo shi daga Roma a shekarar 2017 inda ya ke matsayin dan wasa mafi zura kwallo a kusan kowacce kaka.

Shi ma mai horar da kungiyar ta Liverpool Jurgen Klopp ya bayyana kwallon ta Salah a matsayin wadda za a shafe shekaru 60 duniyar kwallo ba ta manta da ita ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI