Wasanni-Kwallon Kafa

Tottenham za ta maye gurbin Harry Kane da Alvaro Morata

Dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane.
Dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane. JUSTIN TALLIS AFP

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham na shirin sayen Alvaro Morata don maye gurbin Harry Kane, dan wasan da ke kokarin raba gari da kungiyar a karshen wannan kaka bayan gaza cimma jituwar sayar da shi a kasuwar musayar ‘yan wasan da ta gabata.

Talla

Duk da cewa Kane bai samu damar komawa Manchester City a kakar da ta gabata ba, dan wasan ya tabbatar da cewa zai raba gari da Tottenham kafin karewar kwantiraginsa a shekarar 2022.

Shugaban Tottenham Fabio Paratici ya ce dan wasan mai shekaru 28 na jin dadin zamansa a kungiyar yanzu haka, duk da dambarwar da ta dabaibaye shirin sayar da shi a kasuwar musayar 'yan wasan da ta gabata.

Sai dai sanarwar da Tottenham ta wallafa a shafinta ta ce tana fatan sayen Morata wanda yanzu haka ya ke taka leda da Juventus matsayin aro daga Atletico Madrid.

A baya-bayan nan ne Kane ya bukaci Tottenham ta yi gyara a kwantiraginsa don bashi damar iya raba gari da kungiyar gabanin karewar kwantiraginsa tare da kayyade kudin sakinsa kunshe a kwantiragin don saukaka cinikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI