Wasanni - kwallon kafa

Barcelona ta kulla yarjejeniya da Gonzalez har zuwa 2026

Shugaban kungiyar Barcelona Joan Laporta.
Shugaban kungiyar Barcelona Joan Laporta. Lluís Gené AFP/Archivos

Barcelona ta kulla sabuwar yarjejeniyar da dan wasan tsakiyar Spain Pedri Gonzalez, ​​inda zai kasance har zuwa watan Yunin shekarar 2026.

Talla

Jaridar Fabrizio Romano na ƙasar Italiya ta bayyana yarjejeniyar a ranar Laraba a wani sakon Instagram.

A cewar jaridar, sabon kwantiragin ya kai kudi har € biliyan 1, amatsayin mafi tsada a tarihin Barcelona.

Club din tayi cikin Lionel Messi kan Yuro miliyan 700, yayin da Antoine Griezmann ya kuwa aka karbi Euro miliyan 800.

Bayan kammala wannan yarjejeniya da Barca bata bayyana a hukumance ba, kungiyar zata mai da hankali kan tsawaita kwantiragin Ansu Fati da Ousmane Dembele, da kuma Ronald Araujo.

Pedri na cikin mutane goma da aka zaba don kyautar Kopa kuma yana cikin wadanda ke takarar neman Ballon d'Or na wanann shekarar 2021. Kuma shi yaci kyautar gwarzon matashin ɗan wasan a gasar Euro 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI