KENYA - WASANNI

Tauraruwar tseren Kenya Tirop ta mutu bayan daba mata wuka

Tauraruwar  tseren Kenya Agnes Jebet Tirop lokacin da ta samu kambin gudun mita dubu biyar a Stockholm na Sweden 30/ 05/21.
Tauraruwar tseren Kenya Agnes Jebet Tirop lokacin da ta samu kambin gudun mita dubu biyar a Stockholm na Sweden 30/ 05/21. Jonathan NACKSTRAND AFP

Tauraruwar tseren Kenya Agnes Tirop ta kwanta dama ranar Laraba, bayan da aka daba mata wuka a gidanta dake Iten.

Talla

Agnes mai shekaru ashirin da biyar, wacce ta lashe lambar tagulla har biyu a gasa gasan Duniya, ana zargin mijinta ne ya kashe ta.

Wata sanarwa da hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Kenya ta fitar da ke tabbatar da afkuwar lamarin ta ce, ta nuna takaicin mutuwar Agnes Jebet Tirop wanda ta lashe kambun tagulla na duniya a tsaren mita dubu 10.

Humomin kasar suka sun tsinci gawar ‘yar tsaren a  gidansu da ke Iten bayan da mijinta ya caka mata wuka. Amma har yanzu suna gudanar da bincike don gano ƙarin cikakkun bayanai game da mutuwar ta. ”

Tauraruwar tseren Kenya Agnes Tirop.
Tauraruwar tseren Kenya Agnes Tirop. MUSTAFA ABUMUNES AFP/File

Tirop ta kafa tarihi ta hanyar lashe gudun fanfalaki na duniya a shekarar 2015, wanda ta zama matashiya na biyu da ta lashe kambin.

Ta kuma lashe tagulla a tsaren duniya a shekarar 2017 da 2019 a tseren mita 10,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI