Angola-Clasico

Clasico: Wani yaro ya kashe mahaifinsa a Angola

Ronaldo rike da kwallon yana murnan zira kwallo a ragar Barcelona kusa da Víctor Valdés.
Ronaldo rike da kwallon yana murnan zira kwallo a ragar Barcelona kusa da Víctor Valdés. © Reuters

Wani yaro mai shekaru 17 ya kashe mahaifinsa a kasar Angola bisa sabanin ra’ayi tsakaninsu bayan kammala wasa tsakanin Barcelona da Real Madrid a spain.

Talla

A cewar Jaridar Angop a kasar, muhawara ce ta kaure tsakanin mahaifin da dan shi da ke zaune a birnin Luanda, kuma muhawarar ce ta kai ga rasa rai inda yaron ya dauki makami ya rabkawa mahaifin mai shekaru 48.

Dan sandan da ke gudanar da bincike Carlos Andre yace anan take ne mahaifin ya mutu, yaron kuma ya gudu har yanzu ba’a san inda ya shiga ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.