Wasan kwaikwayo

Sauti 20:25
Shagon sayar da fina finan hausa a Najeriya
Shagon sayar da fina finan hausa a Najeriya RFI/salisu

Wasan kwaikwayo na dandali wasa ne da ake gada daga iyaye da kakanni domin nishadi da kuma fadakar da juna dangane da yadda rayuwar yau da gobe ke tafiya a cikin al’umma.

Talla

Amma dangane da yadda zamani ke tafiya, wasan na canzawa tare da rikidewa zuwa wata al’adar wasu al’umma sabanin ta hausawa kuma wannan wata barazana ce ga ci gaban al’adun hausawa, sakamakon shigowar tsarin fina finan bidiyo. Amma duk da haka akwai wadanda ke ta kokarin farfado da wasannin kwaikwayon.

A cikin shirin sai a biyomu domin jin yadda muka tattauna da wasu masu irin wannan sana’a ta raya al’adu a kasashen hausa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.