Cote d’Ivoire ta doke Libya kafin shiga gasar Afrika
Wallafawa ranar:
Kasar Cote d’Ivoire ta doke kasar Libya ci 1-0, kuma Solomon kalou ne ya zira kwallon a raga. Ko a ranar Juma’a dan wasan ya zira kwallo a ragar kasar Tunisia inda aka tashi ci 2-0. A ranar lahadi ne dai kasar Cote d’Ivoire zata fara wasanta da kasar Sudan a gasar cin kofin Afrika da kasashen Gabon da E/Guinea zasu dauki nauyi.
Kasar Libya kuma a ranar Assabar ne zata bude wasa tsakaninta da E/Guinea.
A wata wasan kuma ta zumunta da aka gudanar domin shirya shiga gasar cin kofin Afrika, wasan an tashi ne babu ci tsakanin Gabon da Sudan.
A kasar Spain kuma kasar Morocco ta lallasa kungiyar Grasshopper Zurich ta Switzerland ci 3-1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu