Senegal

Dubban mutanen Senegal sun karrama Bocande

Francois Bocande Tsohon Dan wasan Senegal wanda ya mutu yana da shekaru 54
Francois Bocande Tsohon Dan wasan Senegal wanda ya mutu yana da shekaru 54 AFP

A kasar Senegal daruruwan mutane ne suka yi gangami a babban filin wasan kwallon kafa a Dakar, domin karrama fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Francois Bocande wanda ya mutu a ranar 7 ga watan Mayu a kasar Faransa.

Talla

Shugaban kasar Senegal Macky Sall yana yana cikin tawagar manyan Jami’an gwamnati da suka halarci taron.

A yau Laraba ne dai za’a binnen dan wasan a lardin Casamance.

Tsohon dan wasan Senegal El Hadji Diof da Kalilou Fadiga da Tony Silva sune ‘Yan wasan da suka gabatar da jawabi game da dan wasan a gaban dubun dubatar ‘Yan Senegal.

Beconde dai ya mutu ne yana da shekaru 54 na haihuwa bayan kwashe lokaci mai tsawo yana fama da mutuwar jiki.

Bocande ya taba jagorantar ‘Yan wasan Senegal a gasar cin kofin Afrika, kuma ya buga wasa a kungiyoyin Faransa da suka hada da PSG da Nice da kuma kungiyar Metz inda ya karbi kyautar wanda yafi zira kwallaye a raga a kakar wasa 1985-86.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.