Rikicin Siyasar kasar Mali

Taswirar kasar Mali
Chanzawa ranar: 29/01/2013 - 13:35

A ranar 22 ga watan Maris ne Sojoji suka hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure karkashin jagorancin Kaftin Amadou Sanogo, bayan zargin gwamnatinsa da gazawa wajen magance matsalar tsaro da rikicin ‘Yan Tawayen Azbinawa a yankin Arewacin kasar. A watan Afrilu ne gwamnatin Soji ta Amadou Sanogo ta amince Dioncounda Traore ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya domin shirya zabe cikin kwana 40. Amma juyin mulkin na zuwa ne bayan ‘Yan tawayen kasar sun bayyana karbe ikon wasu daga cikin biranen Yankin Arewaci wanda yafi kasar Faransa girma.