Kamaru

Eto’o ya yi watsi da gayyatar buga wa Kamaru wasa

Samuel Eto’o na Kamaru ya yi watsi da goron gayyatar komawa bugawa kasar shi wasa da kocin kasar ya yi ma shi bayan samun sabani tsakanin shi da hukumar kwallon kafar kasar.

Dan wasan kasar Kamaru Samuel Eto'o a lokacin da yake zantawa da Rediyon Faransa RFI
Dan wasan kasar Kamaru Samuel Eto'o a lokacin da yake zantawa da Rediyon Faransa RFI
Talla

A makon jiya ne kocin Kamaru Denis Lavagne ya hada suna Eto’o cikin tawagar kamaru da za su buga wasa da Cape Verde a wasan neman shiga gasar cin kofin Afrika a ranar 9 ga watan Satumba bayan dakatar da dan wasan saboda ya jagoranci tawayen kin bugawa Kamaru wasa don ba a biya su kudaden lada ba.

A shafin intanet na Eto’o, Dan wasan yace ba zai bugawa kasar shi wasa saboda har yanzu ba sasanta takaddamar da ke tsakanin shi da hukumar kwallon kwallon Kamaru ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI