Duniya

Manyan Kasashen duniya sun yi wa Iran tayin janye takunkumi amma...

Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad.
Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad. REUTERS/Brendan McDermid

Manyan kasashen duniya sun yi wa kasar Iran tayin janye takukumin da suka kakabata muddin ta amince ta dakatar da shirin ta na samun makamin nukiliya, a taron da suka fara yau a kasar Kazakhstan. Su dai manyan kasashen duniyar da ke cikin taron, sun sanar da cewar, za su bai wa Iran damar sayar da zinaren ta da karafa a kasuwannin duniya, da kuma komawa harkokin bankuna muddin ta amince ta yi watsi da shirin samun makamin nukiliya, wajen takaita tace sinadarin uranium. 

Talla

Mai magana da yawun Babbar jami’ar diplomasiyar kasashen Turai, Catherine Ashton, wato Tien Shan, ya ce sun yi kyakyawan shiri dan ganin an cim ma yarjejeniya a taron na kwanaki biyu.

Sai dai a bangare guda, jagoran tawagar Iran a taron, Saeed Jalili, ya ce ba za su amince da wata yarjejeniyar da ta sabawa muradun kasarsu ba.

Shi kuwa Mataimakin Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Ryabkov, ya ce fatarsu shi ne tattaunawa maimakon bayar da sharudda, inda ya bukaci bangarorin biyu da su kaucewa bata lokaci wajen tattaunawa ta fahimtar juna.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI