Kamfanin Thomas Cook zai kori ma’aikata 2,500
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kamfanin sufuri na Thomas Cook dake kasar Birtaniya ya sanar da cewa zai zaftare guraban aiki da yawansu ya kai 2,500, a matsayin yunkurin yin garanbawul ga kamfanin.
A cewar Kamfanin wadanda zaftarewan zai shafa sun hada da ma’aikatan kula gudanarwa, wanda hakan zai yanke kashi 16 daga cikin 100 na yawan ma’aikata da suka kai 15,000 a Birtaniya da Ireland.
Wannan labari rage ma’aikatan ya z one kwanaki biyu bayan kamfanin ya bayyana rufe ofishinsa dake kasar Faransa.
Kamafanin dai bayyana asarar da ya tafka na kudin Euro 586 miliyan a watan Nuwambar bara a bisa dalilin tabarbarewar tattalin arzikin wasu daga cikin kasashen Nahiyar Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu