Najeriya

Kungiyar Ansaru ta wallafa hoton bidiyon ‘Yan kasashen wajen da ta kashe a yanar Gizo

'Yan kungiyar Ansaru a Najeriya
'Yan kungiyar Ansaru a Najeriya ds2.ds.static.rtbf.be

Kungiyar Ansaru da ake zargin ta kashe ‘Yan kasashen wajen da ta yi garkuwa da su a kwanakin baya, ta wallafa hotan bidiyon gawawwakin mutane bakwan da ta kashe a shafin yanar gizo. Tun a watan Febrairun daya gabata ne kungiyar ta yi garkuwa da mutanen su bakwai da suka hada da dan kasar Italiya, Girka da Birtaniya dai dai da kuma wasu ‘Yan kasar Lebanon su hudu a wani Kamfani da ake kira Setraco dake garin Jama’are a Jihar Bauchi dake Tarayyar Najeriya. 

Talla

A jiya ne dai Sakataren Harkokin wajen kasar Birtaniya William Hague ya ce akwai yiwuwar an kashe mutanen da ake garkuwa da su, abinda ya kwatanta a matsayin rashin imani.

Koda yake har izuwa yanzu hukumomin Jihar ta Bauchi basu musanta ko tabbatar da aukuwar wannan lamari ba.

Shi dai hotan bidiyon a cewar rahotanni ya nuna cewa a ran 9 ga watan Maris aka daukeshi, ya nuna wani mutum dauke da bindiga kusa da wasu tarin gawawwaki, sannan sai kuma aka nuna fuskokinsu wanda fitila ta haska.

An kuma rubuta da harshen larabci cewa “wannan shine kisan mutane bakwai mabiya addinin Krista a Najeriya.”

Kana a kasa aka kuma rubuta da harshen larabci da Ingilishi cewa “da sunan Allah mai rahama mai jin kai.”

Tun bayan yin garkuwa da mutanen ne, kungiyar ta Ansaru ta dauki alhakin yin hakan inda ta bayyana cewa ta yi hakan ne saboda irin muzgunawa addinin Islama da ake yi a kasashe duniya irinsu Afghanistan da Mali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.