Syria

Rasha ta aika da taimakon abinci da barguna mai yawan tan 10 zuwa Syria

Wani yanki da aka kai hari a Syria
Wani yanki da aka kai hari a Syria REUTERS/Muzaffar Salman

Kasar Rasha ta aika da abinci da barguna da yawansu ya kai tan 10 zuwa kasar Syria, waccec babbar kawace ga kasar ta Rasha. “Wani jirgin kasar Rasha ya sauka a filin saukan jirage na Bassel al- Assad a yau Talata, dauke da abinci da barguna da yawansu ya kai tan 10.” Kamfanin Dillancin labarai na SANA ya bayyana.  

Talla

Taimakon na yau shine karo na biyar ke nan da kasar ta Rasha ke aikawa kasar ta Syria wacce a yanzu haka take fama da rikicin da ya doshi shekaru uku, a cewar SANA.

Kasashen Rasha da China sun kasance kasashe biyu da suka hau kujerar naki a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya akan yunkurin daukan mataki akan gwamnatin Assad.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.