Iran-Amurka

Iran na ci gaba da kulla kawance a yankin Latin Amurka

Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmadinejad
Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmadinejad REUTERS/Asmaa Waguih

Kasar Iran na ta kokarin kulla kawancen gaske da wasu kasashen Latin Amurka da suka damu da halin kane-kanen da kasar Amurka ta yi ga al’amurran Duniya. Sai dai babban jami’in Sojin kasar ya ce Iran ba wani tasiri za ta yi a yankin ba.  

Talla

Janar John Kelly, Shugaban Rundunar Sojin kasar Amurka ta yankin kudanci, ya ce gaskiyar al’amari anan shine kasar Iran na nan tana kokarin inganta dankon zumunci da wasu kananan kasashe dake adawa da kasar Amurka a yankin.

Yanzu haka dai Iran ta shiga kulla huldar Diplomasiyya da tattalin arziki da kasashe irin su Venezuela, da Bolivia da Ecuador da Argentina, abinda ake ganin zai haddasa kyamar kasar Amurka a yankin an Latin Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI