Kwallon kafa

Roy Hodgson ya jinjinawa Owen

Mai horar da 'Yan wasan Ingila, Roy Hodgson
Mai horar da 'Yan wasan Ingila, Roy Hodgson

Mai horar da ‘Yan wasan kwallon kafar kasar Ingila, Roy Hodgson ya jinjinawa tsohon dan wasan kasar ta Ingila, Michael Owen, wanda ya bayyana cewa zai yi bankwana da buga kwallo a karshen wannan kakar wasa, inda ya ce kwallayen da Owen ya zirawa kasarsa abu ne da ya cancanci a yaba.

Talla

Owen dai ya zira kwallaye 40 a wasanni 89 da ya bugawa Ingila, ya kuma taba lashe kyautar zakaran duniya a fagen wasan kwallon kafa ta Ballon d’Or a shekarar 2001.

Sai dai Owen daga baya ya yi fama da jinyar raunuka a rayuwarsa ta kwallo.

“Kwallayen da Owen ya zirawa Ingila guda 40 a wasanni 89 abu ne mai matukar muhimmanci ga tarihin kwallon kafa a Ingila.” Inji Hodgson.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.