Kwallon kafa

Najeriya ta sha da kyar a hanun Kenya da ci 1-1

'Yan wasan Najeriya
'Yan wasan Najeriya

Najeriya ta sha da kyar a karawar da suka yi da Kenya inda aka tashi a wasan na neman shiga gasar cin kofin duniya da ci 1-1. Nnamdi Oduamadi ne ya farkewa Najeriya kwallonta a yayin da ya rage mintina uku kacal a kammala wasan, wanda Kenya ta yi nasarar zira kwallo a farkon wasan.  

Talla

Ita kuwa makwabaciyar Najeriya, wato kasar Nijar ta sha mamayane a hanun Burkina Faso wacce ta zo ta biyu a gasar nahiyar afrika da aka kammala da ci 4-0.

Kuma dan wasanta Jonathan Pitropa ne wanda ya lashe kyautar zakaran dan wasa a gasar nahiyar afrika ya zira kwallaye biyu daga cikin kwallaye hudun.

Kasar Kamaru kuwa ta baje ikonta ne a gida, bayan dan wasanta Samuel Eto’o ya zira kwallaye biyu, inda aka tashi da 2-1, a yanzu haka kuma Kamaru ce ke jagorancin rukuninsu.

Ita ma dai Afrika ta Kudu, ta taka rawar gani ne da ci 2-0 akan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, a yayin da Mali ta doke Rwanda da ci 2-1, kana Mozambique da Guinea suka tashi canjaras, a dai dai lokacin da Lesotho da Zambia suka ta shi da ci 1-1.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.