Afrika ta Kudu

Mandela na samun sauki – Shugaba Zuma

Tshohon shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela
Tshohon shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela Reuters

Fadar gwamnatin Afrika ta kudu ta ce tsohon Shugaba Nelson Mandela yana samun sauki daga rashin lafiyar huhu da yake fama da ita inda a yau Litinin Tshon shugaban ya kwashe kwanaki biyar ke nan a gadon Asibiti.

Talla

Dan shekaru 94, Mandela na ci gaba da samun kula bayan likitoci sun janye wani ruwa da ya mamaye gefen huhunsa.

Tsohon shugaban kasar dai ya samu addu’oi daga dumbin mabiya bayansa bayan wannan rashin lafiya da ta kama shi, a yayin da a san ranar da za a sallame shi ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI