Wasan Tennis

Murray da Serena sun lashe gasar Miami Masters

Andy Murray
Andy Murray REUTERS/Daniel Munoz

Andy Murray, dan kasar ingila ya lashe kofin gasar Miami Masters bayan ya doke David Ferrer dan kasar Spain a wasan karshe da aka kara a jiya Lahadi. 

Talla

Murray a yanzu haka ya lashe gasa daban-daban har guda 26. Yanzu haka Murray ya dane matsayi na biyu a jerin ‘yan wasan da suka fi iya wasan Tennis a duiniya.

A bangaren mata kuwa Serena Williams ta doke Maria Sharapova ne a wasan karshe na Miami Masters, wannan kuma shine karo na shida da Williams ke lashe wannan gasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI